1 - Kar ka sayi coin sai kayi bincike a kai, akwai coins ɗin da suka haramta a musulunci ka saye su, kamar waɗanda ke ta'ammali da riba, ƙungiyoyin mafia, maɗigo da luwaɗi da sauran su, ta hanyar bincike ne kaɗai zaka gane irin waɗannan coins din, ka tabbatar ka karanta whitepaper ɗin project ɗin da kyau, ka san manufar su, domin komai ka samu na kudi za'a tambaye ka ta hanyar da ka same shi ranar tashin ƙiyama, sai mu kula.

2 - Kar ka yarda ka saka kuɗin aro ko bashi a crypto, in zaka zuba kuɗi ka tabbatar naka ne, don kar a samu matsala a zo ana kace nace da kai, wataƙila ma maganar ta kai gaban kotu, don haka, ko kuɗin mahaifin ka ne kar ka sa su ba tare da izinin shi ba, domin kuɗi da kake iya gani suna iya haɗa faɗa tsakanin ɗa da mahaifi.

3 - Ka zuba abinda zaka iya jure rashin shi, kar ka zuba kuɗaɗen da ka san in ka rasa su zaka yi dana sani, ko kuma ka kasa barci, ko a tsince ka a gadon asibiti. Ka tabbatar da cewa kuɗin da zaka zuba a crypto ka fi ƙarfin su, kuma ko da ka rasa su baka da matsala. Misali : kana da ₦100,000 a shawarce ya kamata ka zuba kamar ₦10,000 ko ₦20,000 haka.

4 - Kar ka bari kwaɗayi da dogon buri ya sa ka ƙi sayar da coin bayan ya baka riba, ka tabbatar ka cire kudin ka da ka sa da wani ɓangare na riba a karon farko da coin din zai baka riba, sai dai in holding zaka yi.

5 - Haƙuri shi ne mabuɗin nasara a komai, a crypto ma in baka da haƙuri ba zaka iya samun kuɗaɗe masu yawa ba, sai dai ka samu na shan ruwa. Don haka ne nake bawa ƴan baiwa shawarar juriya da rungumar holding fiye da trading.

6 - Ka tabbatar da cewa ka san me kake yi, wato ka yanke shawarar me zaka yi, ko dai trading, ko kuma holding, kar ka shiga kasuwa ba tare da ka samu tabbacin abinda kake son yi a kasuwar ba, zaka iya yin asara maimakon riba. Haka nan, yana da kyau ka ɗaura target akan ko wane coin da ka saya. Misali : Bayan ka gama binciken ka akan Bitcoin, sai ka gano cewa zai iya kaiwa $1,000,000, to ka tabbatar da cewa ka ƙayyade lokacin fitar ka daga kasuwar, ko dai kafin a kai wannan farashin ko kuma in an kai.

7 - Kar ka yarda da coin ɗaya kaɗai : Abun nufi kar ka ɗaura wa coin ɗaya kaɗai soyayya, shi kaɗai zaka zuba wa kudi, ta yadda in yayi failing kai ma ka yi failing kenan. Ka yi duk mai yiwuwa wurin samun coins masu inganci kar ka dogara da guda ɗaya, musamman in holding zaka yi. A taƙaice (Diversify your portforlio).

8 - Kar ka dogara da Crypto kaɗai a matsayin sana'a, duk yadda kake samun kuɗi ta ita. Ka tabbatar kana da wasu harkokin na zahiri da kake ɗaukar ribar ka ta crypto kana zubawa ciki.

9 - Duk coin ɗin da ka ga yayi tashin gwauron zabi kar ka yarda ka shige shi a irin wannan lokacin, idan ba haka ba zaka zama exit liquidity, waɗanda kasuwa za ta ƙare a kan su, su ba su ci riba ba sai dai asara.

10 - Duk irin abunda mutane zasu faɗa game da coin ɗin da kake riƙe da shi, kar ka yarda ka biye musu, in dai ka yarda da abinda kake riƙe da shi, kuma ka yarda da binciken ka, in ba haka ba za su kai ka su baro ka. Ko waye ne ya faɗi magana kar ka ɗauke ta a matsayin financial advice, ka je ka yi bincike tukuna (Do Your Own Research).

11 - Kamar yadda ake samun riba ake kuma faduwa a kasuwar zahiri, haka ma Crypto take, kar ka yarda da huɗubar wasu da ke nuna maka daɗin abun kaɗai, lallai ana cin riba kuma ana faɗuwa a crypto kamar ko wace kasuwa, don haka ka shirya, crypto ba platform bane, kasuwa ce kamar ko wace kasuwa, kuma akwai haɗarin rasa kuɗaɗen ka gaba ɗaya in baka da ilimi a kan ta.

12 - Kar ka zauna wuri guda baka bincike da karatu. Ka tabbatar ka karanci crypto kafin ka fara, kuma duk abunda baka sani ba kayi bincike gami da tambayoyi don sanin haƙiƙanin abun, rashin yin haka na iya sa ka tabka asara mai yawan gaske.

13 - Ba a dare ɗaya ake yin kudi ba. Kar ka rudu da cewa wane yayi kudi da Crypto kai ma ka ƙwallafa rai lallai lallai daga shigowar ka sai ka samu kuɗaɗe masu yawa ko ta halin yaya, arziki na Allah ne, kai dai ka cigaba da nema.

14 - Ba kudin banza ake ci a crypto ba, crypto ba caca bane, kasuwanci ne, babu free money a crypto, duk wanda ka ga ya samu kudi tabbas ya sha wahala, ba a crypto kaɗai ba, ko a ina ne, idan ma bai sha wahalar ba, to wani ya sha a madadin shi. Ba a samun kuɗi a banza.

Allah ya sa mu dace.

Kar a manta da joining na Telegram channel namu. t.me/imaamng

✍️ Ibrahim Imaam

(LIMAMIN ƳAN BAIWA)

#Limaminkirifto