1 - Kar ka sayi coin sai kayi bincike a kai, akwai coins ɗin da suka haramta a musulunci ka saye su, kamar waɗanda ke ta'ammali da riba, ƙungiyoyin mafia, maɗigo da luwaɗi da sauran su, ta hanyar bincike ne kaɗai zaka gane irin waɗannan coins din, ka tabbatar ka karanta whitepaper ɗin project ɗin da kyau, ka san manufar su, domin komai ka samu na kudi za'a tambaye ka ta hanyar da ka same shi ranar tashin ƙiyama, sai mu kula. 2 - Kar ka yarda ka saka kuɗin aro ko bashi a crypto, in zaka zuba kuɗi